For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Karamar Hukuma Za Ta Hana Ma’aikata Albashi Saboda Rigakafin Korona A Jigawa

Majalissar Karamar Hukumar Garki da ke jihar Jigawa ta bayar da umarnin rike albashin duk ma’aikacin da ba aiwa rigakafin korona ba.

Shugaban Karamar Hukumar Garki, Alh. Mudassir Musa ne ya bayar da umarnin ne a lokacin kaddamar da rundunar yaki da cutar Korona ta karamar hukumar.

Ya bayyana cewa, duk ma’aikacin karamar hukumar ta Garki da bai nuna katin shaidar yin allurar rigakafin Korona ba, ba za a biya shi albashin watan Disamba ba.

A baya dai, gwamnan jihar Jigawa Muhammadu Badaru Abubakar ya bayar da umarni ga dukkan shugabannin kananan hukumi 27 na jihar da su tabbatar da cewa yawan rigakafin da akai a jihar ya kai Miliyan 3.6 kafin 24 ga watan Disamba.

Comments
Loading...