Jam’iyyar APC na fama da kararrakin da ba su gaza 208 ba a kotuna daban-daban, inda wadansu daga cikinsu ke kalubalantar shugabancin jam’iyyar a jihohi da dama, wasu kuma ke kalubalantar sahihancin Kwamitin Riko na Shugabancin Jam’iyyar na Kasa.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa, ƙararrakin tare da wadansu ƙorafe-ƙorafen na neman a rushe duk zaben da akai na jihohi ƙarƙashin jagorancin Kwamitin Riko na Jam’iyyar, abin da zai iya jawo tsaiko ga Babban Taron Zaben Shugabannin Jam’iyyar na Kasa da aka shirya gudanarwa ranar Asabar 26 ga watan Maris, 2022.
Wannan matsala ta sake baiyana ne a ranar Alhamis, lokacin da Yusuf Ali, mai temakawa Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni kuma Shugaban Kwamitin Rikon Jam’iyyar APC na Kasa ya sanar da wakilin PUNCH cewa har yanzu Mai Mala Buni ne Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa.
A dai ranar 25 ga watan Yuni na shekarar 2020 ne, a wani zama da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta, Mai Mala Buni ya zama Shugaban Kwamitin Rikon Jam’iyyar APC na Kasa, inda a wannan zaman jam’iyyar ta bukaci duk masu ƙararraki a kanta a kotuna da su janye.
Domin nuna wannan umarni na jam’iyyar na gaske ne, Shugabancin Jam’iyyar a zamansa na ranar 8 ga watan Disamba, 2020, ya sanar da korar tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Kudu maso Kudu, Hilliard Eta saboda shigar da jam’iyyar kara da yai yana kalubalantar ruguje Shugabancin Jam’iyyar wanda Adams Oshiomhole ya jagoranta.
Wata takarda da jaridar PUNCH ta samu ta nuna cewa, cikin shekara daya da ta gabata kadai an shigar da APC kara a kotu kan ƙorafe-ƙorafe 208.
A wasu ƙararrakin, masu ƙarar sun sami odar kotu da ke dakatar da jam’iyyar daga yin Babban Taron Zaben Shugabanni na Kasa, ko kuma dena kiran wasu shugabannin jam’iyyar na jihohi a matsayin shugaban in.