Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce Hukumar Tara Haraji ta Tarayya (FIRS) za ta ci gaba da karbar Harajin (VAT) bayan hukuncin Kotun daukaka kara kan lamarin.
Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a birnin New York yayin da yake magana kan rashin jituwa a harkar karbar harajin VAT tsakanin FIRS da Gwamnatin jihar Ribas.
Babban Lauyan Gwamnatin ya yi bayanin cewa hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke na cewa FIRS da Gwamnatin Ribas su bar abu a yanda yake, ya baiwa Hukumar Tattara Haraji (FIRS) damar ci gaba da karba.
Ya ce Hukumar Tattara Haraji (FIRS) ce ta ke tara harajin kafin rigimar ta taso, wanda a kan haka gwamnatin Ribas ta tunkari babbar kotun.
Malami ya ce “Matsayin ba na Gwamnatin Tarayya kadai ba ne, amma hakika ra’ayin bangaren shari’a shine, ya kamata a kiyaye tsarin da a ke da shi kan karbar harajin.”
“Kuma dangane da tsarin shari’a, halin da ake ciki a lokacin da bangarorin suka tunkari kotun, hukumar FIRS ce ke tattara harajin da ake tarawa.
“Sanin haka, Gwamnatin Tarayya ta yi nasarar samun umarnin da ke tabbatar da ingancin halin da ake ciki, wanda matsayin shi ne cewa Hukumar FIRS ta ci gaba da tattara harajin.
“Hakan zai ci gaba da kasancewa har zuwa lokacin da kotu za ta yanke hukunci kan kararrakin da jihohi suka gabatar gabanta, musamman gwamnatin jihar Ribas da gwamnatin jihar Legas.”
A baya NAN ta rawaito cewa gwamnatin Ribas ta bukaci Kotun Koli da ta yi watsi da hukuncin Kotun Daukaka Kara na ranar 10 ga Satumba da ke ba da umarnin cewa gwamnatin Ribas da FIRS su ci gaba da kasancewa kan tsarin karbar harajin da aka sani.
Kwamitin mutune uku na Kotun Daukaka Kara karkashin jagorancin Haruna Tsammani, ya gabatar da umurnin da gwamnatin ta Ribas ta kalubalanta a Kotun Koli.
Jihar ta kuma bukaci Kotun Kolin ta rusa kwamitin kotun daukaka kara, wanda ya ba da umarnin wucin gadin tare da ba da umarnin a kafa wani don sauraron karar.
“Amma wani abin sha’awa shi ne cewa lallai Gwamnatin Tarayya ta fahimci cewa a lokacin da ake takaddama tsakanin Gwamnatin Jiha da ta Tarayya, Kotun Koli ce ya kamata ta kasance tana da ikon yanke hukunci kan takaddamar da ke tsakaninsu.
“Kuma muna daukar kokari na samar da wani yanayi da zai sa Kotun ta yanke hukunci gaba daya a kan lamarin”, in ji Malami.
(NAN)