Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta amince da rigakafin zazzabin cizon sauro (malaria) karo na farko a tarihi.
Kwararru a hukumar ta WHO sun bayyana cewa, rigakafin za ta temaka wajen ceto dubannan mutane duk shekara.
An samu nasarar gwada rigakafin a kasashen Ghana, Kenya da Malawi in ji WHO.
Hukumar WHO ta ce za a rarraba rigakafin a kasashen Africa masu fama da zazzabin cizon sauro da kuma sauran kasashen sauran nahiyoyi da ke da matsalar zazzabin.
“Rigakafin da aka dade ana jira domin yara wata babbar nasara ce a fannin kimiya, lafiyar yara da kuma kula da zazzabin cizon sauro, haka kuma zai ceci dubannan yara duk shekara,” In ji Tedros Adhanom Ghebreyesus, Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya, a wata hira da akai da shi ranar Larabar nan.