Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya ce cikin watan da ya gabata, kasashe matalauta sun yi watsi da allurar rigakafin cutar Korona sama da miliyan 100 da gidauniyar COVAX ke rabawa, saboda yadda allurar ke daf da lalacewa.
Kididdiga mai yawa ta nuna wahalhalun da ke tattare da yin allurar rigakafin a duniya duk da karuwar samar da alluran rigakafin, tare da COVAX yana kusa da isar da allurar rigakafi biliyan 1 ga jimillar kasashe kusan 150.
Babban daraktan sashen samar da kayayyaki a hukumar ta UNICEF Etleva Kadilli, ya shaida wa ‘yan Tarayyar Turai cewar babban dalilin kasashen marasa karfi na kin karbar tallafin rigakafin na Korona shi ne yadda alluran ke shirin lalacewa nan da ba da dadewa ba.
KU KARANTA: Majalissar Wakilai Ta Amince Da Kudirin Kulawa Da Lafiyar Yara Kyauta
Babban jami’in na UNICEF ya kara da cewar, akasarin kasashen matalauta na fama da kalubalen tilasta jinkirta rabawa al’ummominsu alluran rigakafi na Korona saboda rashin isassun wuraren ajiya ciki har da na’urar sanyaya kaya ta firji domin adana alluran na rigakafin.
Bayanai daga hukumar UNICEF sun nuna cewa, yanzu haka akwai allurai akalla miliyan 681 na tallafi da aka yi jigilarsu kasashe matalauta kusan 90, kamar yadda wata kungiyar agaji ta CARE ta tabbatar a baya bayan nan.
Daga: RFI Hausa