Alkaluma sun nuna cewa, kawo yanzu kaso 4.2% kawai aka gama yiwa rigakafin Korona a Najeriya duk da kiraye-kiraye da kuma dokokin da gwamnatoci ke sa wa don ganin an wuce hakan.
Wadannan alkaluma sun kuma nuna cewa, a dai-dai ranar Lahadin jiya, wadanda suka karbi zagayen farko na rigakafin Korona a Najeriya, kaso 9.8% na yawan ‘yan kasar.
Hukumar Hana Yaduwar Cututtuka ta Najeriya, NCDC, a bayanan da take saki kullum-kullum, ya nuna cewa, ana samun karuwar masu kamuwa da Korona a Najeriya, yayin a satin farko na watan Janairu aka samu mutuwar a kalla mutune 38.
KU KARANTA: Karamar Hukuma Za Ta Hana Ma’aikata Albashi Saboda Rigakafin Korona A Jigawa
Duk da wannan matsala, har yanzu akwai jihohin da ba su yiwa mutanen da suka kai 200,000 rigakafin Korona ba, yayin da jihohin Abia, Kogi da Niger ba su ma fara yin zagaye na uku na rigakafin ba.
Kididdigar da wakilin PUNCH yai ta nuna cewa, duk da wasu jihohin sun fara zagaye na uku na rigakafin, jihohin Akwa-Ibom, Anambra, Benue, Ebonyi, Imo, Kwara, Sokoto da Yobe har yanzu ba su yiwa mutanen da suka 100 rigakafin ba a zagaye na uku.
Yayin da a jihar Imo aka yiwa mutum goma kacal a zagaye na ukun, jihar Ebonyi ita kuma ta yiwa mutum 52, jihar Akwa-Ibom kuma ta yiwa mutum 67.
Hukumar Bunkasa Lafiya a Matakin Farko ta Kasa, NPHCDA, ta gargadi jihohi da su tashi tsaye wajen ganin an yiwa mutane da yawa rigakafin Korona, a kokarinta na ganin an magance cutar.
NPHCDA ta yi kira ga gwamnoni da su kirkiri dokoki su kuma tilasta karbar rigakafin Korona ga ma’aikatan jiha da na kananan hukumomi a jihohinsu.