Gidauniyar Tunawa da Mallam Adamu Majia ta amince da bayar da tallafin karatu na kashi 50 cikin 100 ga dalibai ‘yan asalin jihar Jigawa da suka cancanci karantun digiri na farko a Khadija University, Majia.
Haka kuma, Gidauniyar ta kuma amince da ragin kudin shiga makarantar da kashi 30 cikin 100 ga masu karatun digirin farkon ‘yan asalin jihar Kano.
Gidauniyar ta yi wannan ragi ne, ga daliban da za su yi a karatu a shekarar karatu ta 2021/2022.
Shugaban Gidauniyar, Alhaji Musa Adamu Majia ne ya sanar da hakan a wani jawabi da ya raba.
KU KARANTA: Duk Da Kalubale Ban Gajiya Wajen Cika Burin Matasan Mazabata Ba – Magaji Da’u Aliyu
Alhaji Musa Adamu, wanda shine wanda ya kirkiri jami’ar Khadija University, Majia ya ce, wannan sauki ya zo daidai da kudirin Gidauniyar wajen bayar da gudunmawa a cigaban ilimin jihar Jigawa, Kano da ma kasa baki daya.
A baya dai, Gidauniyar ta sanar da yin karatu kyauta ga duk dan garin Majia wanda ya cancanci shiga jami’ar.
Darussan jami’ar a matakin digiri na daya, sun hada na tsangayar ilimin rayuwar dan’adam, kimiyya, harkokin lafiya, lissafi da kuma sauransu.
Sanarwar ta kuma bukaci wadanda suka cancanci shiga jami’ar a fadin Najeriya, da su ziyarci shafin jami’ar a www.kum.edu.ng domin neman damar karatun, ko kuma su kira lambar Rijistaran jami’ar, Dr. Aliyu Shehu, 08034387460.