Shugaban Majalissar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan ya baiyana cewa, ko bayan zaɓen shekarar 2023, Shugaba Buhari ne zai ci gaba da baiwa jam’iyyar APC shugabanci.
Sanata Ahmad Lawan ya baiyana hakan ne a daren jiya Asabar, lokacin da yake jawabi a Babban Taron Zaɓen Shugabannin Jam’iyyar APC na Kasa wanda aka gudanar a Eagle Square da ke Abuja.
Ya ce, ƙoƙarin Buhari na tabbatar da haɗin kai a cikin jam’iyyar duk kuwa da tarun matsaloli, ya ba shi damar kasancewa fitilar da ake buƙata wajen saita jam’iyyar a kowanne lokaci.
“Bari na faɗa ƙarara; ba za ka zama a takardar zaɓe ba a 2023, amma zaka ci gaba da kasancewa fitila kuma ma’auni na gaskiya ga APC ko bayan wa’adinka ya ƙare,” in ji Ahmad Lawan.