
Labarin Lionel Messi a gasar cin kofin duniya ya kusa zuwa karshe, ko in ce ya ma zo karshe, amma dai nasan abubuwa za su rage dadi idan babu Messi.
Kalaman tsohon dan wasan Ingila kenan Gary Lineker, wanda kuma yake sharhin wasanni a BBC.
Ko me zai faru a ranar Lahadi a wasan karshe na World Cup, wanda zai kasance zuwansa gasar kenan na karshe a matsayin dan wasa, kokarin Messi a Qatar ya kara tabbatar da digadigan Messi cikin zuciyar masu kaunarsa a fadin duniya.
An ji wani yanayi mai dadi bayan da Argentina ta yi nasara a wasan kusa da na karshe kan Croatia, wanda wata ‘yar jarida ta shaida wa Messi cewa ka sanya farin ciki a fuskar mutane masu yawa, kuma mafi zama abun jin dadi shi ne idan ya yi nasara a wasan karshe da Faransa.
Ta yi gaskiya, domin ni kaina mutane sun sha tambayata cewa ” sau nawa ka taba yi wa Messi mgana” Ban taba jin ba dadi ba domin ganin Messi yana sanyawa na ji farin ciki kuma na kusa shekara 20 ina jin hakan.
Yanzu shekararsa 35, kuma bai yi nadamar wadannan shekarun da ya kwashe ba yana buga kwallo.
BBC Hausa