Tsohon Gwamnan jihar Jigawa kuma jigo a jam’iyyar PDP, Sule Lamido, ya bayyana yunkurin tabbatar da kudirin dokar zaben da za ta sa jam’iyyu gudanar da zabe ta bin tsarin ‘yar tinke a matsayin yin hawan kawarawa ‘yancin jam’iyyu a Najeriya.
Sule Lamido, ya bayyana hakanne a shafinsa na facebook a ranar Laraba, a wani dogon rubutu da yaiwa take da ‘Sanatocin APC ko na Mulkar Jam’iyyu ne Kamar Yanda Marigayi Air Marshal Alfa ya Kasancewa SDP da NRC?
Sule Lamido na mayar da martani ne ga kudirin dokar zabe da zai tabbatar da cewa dole jam’iyyu su gudanar da zaben cikin gida ta bin tsarin direct primaries (‘yar tinke).
Ya ce, “na fahimci cewa, Majalissar Dattawan da APC ke rinjaye ta yi dokar da za ta sa dole jam’iyyu su gudanar da zaben cikin gida ta bin tsarin ‘yar tinke domin zabar ‘yan takarkaru.
“Bayan kuma kundin tsarin mulkin Najeriya ya kare tsarin demokaradiyarmu wanda kuma ya bayar da damar jam’iyyu su tsara gudanar da kansu ya kuma dorawa Hukumar Zabe mai Zaman Kanta alhakin kulawa da yanda jam’iyyun ke biyayya ga kudin tsarin mulkin nasu wanda hukumar zaben ke da su?”
“Yanzu kuma Majalissar Dattawa ta APC ta mayar da kan ta wata mai mulkin mallakawa jam’iyyu zai zama wani abu na kokarin ceton kai da makomar jam’iyyar APC ke nema.”
“Gaskiya ne, a lokutan gwagwarmayar tasowar siyasarmu akwai lokacin da muke da jam’iyyun da Marigayi Air Marshal Alfa ke mulkar SDP da NRC, amma wannan ya faru ne lokacin da ya kasance, jam’iyyun, kirkirarsu da gudanar da su duk gwamnati ce ke yi.
“Ta samar da cikakkun ofisoshi a kasa, jihohi, kananan hukumomi da kayan ofis da ma motoci, babura da wadataccen kudin gudanar da aiyukan jam’iyyu da suka hada da na zirga-zirga da masauki lokacin tarurrukan jam’iyyun – ku yanzu me kukai?
“Kawai ku ce jam’iyyu ba su da ikon kansu kawai mun zama wani sashi na gwamnati, kuma duk mun san abun da hakan zai jawo.
“To yanzu idan har wannan dokar ta tabbata, Majalissar Dattawan za ta tanadar da kudaden da ake bukata ga kowacce jam’iyya domin ganin ta bi dokar?
“Lokacin da Sanatocin APC ke jin cewar suna da karfin yin doka, ya zama dole su san cewa nauyi ne a kansu su tabbatar da cewa dokokinsu sun sami amincewar kowa.
“A wannan yanayi, jam’iyyar PDP ya kamata ta samar da duk abin da ake bukata wajen kalubalantar wannan sashin doka a kotu.”