A yau Juma’a, kasar Koriya ta Arewa ta yi gwajin wani sabon makami mai linzami wanda ke iya kakkabo jirgin sama, a daidai lokacin da Kwamintin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ke shirin gudanar da zama domin mayar da martini ga Koriyar.
RFI Hausa ta sanar da cewa, sabon gwajin na zuwa ne gabanin zaman Kwamitin Tsaron na Majalisar Dinkin Duniya domin nazari kan wani gwajin na dabam da Koriya ta Arewar ta yi a farkon makon nan, lamarin da ya haddasa cece-kuce.
Makamin da Koriyar ta harba a yau, na da matukar karfin yaki, baya ga wasu sabbin fasahohi da aka makala masa kamar yadda Kamfadin Dillancin Labaran Kasar ya rawaito.
Wani hoto da Jaridar Rodong Sinmun ta wallafa ya nuna makamin mai linzamin na lulawa can sararin samaniya bayan an cilla shi daga cibiyarsa.
Wannan dai na a matsayin takala ta baya-bayan nan da Koriyar ta yi bayan sassaucin da ta yi domin ganin kamun ludayin gwamnatin shugaba Joe Biden na Amurka.