For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Kotu Ta Ɗaure Wani Likita Shekaru 27 Saboda Yin Damfara

Alkali Abdulazeez Anka na Babbar Kotun Tarayya da ke Ikoyi a Jihar Lagos, ya ɗaure wani likita ɗan Najeriya kuma ɗan Amurka, John Nweke, shekaru 27 a gidan gyaran hali, saboda samunsa da laifin damfara.

Nweke ya fuskanci wannan hukunci ne saboda ya damfari shagon siyar da kayayyaki ta yanar gizo mai suna Konga Online Shopping Limited.

Kayayyakin da aka ce ya sata sun haɗa da tsala-tsalan wayoyin hannu na zamani guda 19 da kuma kemarori guda 2 wadanda aka ƙiyasta kuɗinsu naira miliyan 35.

Mai magana da yawun ƴansandan na ɓangaren Kula da Damfara na Jihar Lagos, Eyitayo Johnson, a wata sanarwa da ya fitar ranar Larabar nan ya ce, an kama wanda ake zargin ne tun shekarar 2016.

Tun a ranar 14 ga watan Fabarairu na 2022 ne a gaban alkali, aka kama wanda ake zargin da laifin kuma aka yanke masa hukunci daurin shekaru 27 ba tare da zaɓin tara ba.

Haka kuma an umarce shi da ya dawo da kudaden da ya damfara ga wadanda ya damfara.

An kama Nweke tare da wadanda sukai damfarar tare wadanda biyu a cikinsu sun mutu yayinda ɗaya ke raye a halin yanzu.

Comments
Loading...