Babbar Kotun Gwamnatin Tarayya da ke zamanta a Kano ta ki amincewa ta yi kwarya-kwaryar hukuncin da kamfanin Coca-Cola ya nema na dakatar da Pop Cola cigaba da kasuwanci har sai an kammala shari’ar da ake yi.
A lokacin da yake yanke hukuncin a ranar Laraba, Alkali Muhammad Nasir Yunusa ya umarci gaggauta cigaba da sauraron karar.
“Duk da yana daga cikin damar da wannan kotu take da shi na yin kwarya-kwaryar hukunci a kan kara, amma a irin wannan shari’ar, yana da muhimmanci ga alkali ya saurari dukkan hujjoji daga dukkanin bangarori domin baiwa kotu damar yin hukunci na adalci a karshen shari’ar.
“Ina bayar da umarnin gaggauta sauraron wannan kara maimakon yin kwarya-kwaryar hukunci,” in ji Alkali Yunusa.
Idan za a iya tunawa, kamfanin Coca-Cola ya shigar da kamfanin Mamuda Beverages Nigeria Limited, masu yin Pop Cola zuwa kotu kan rigimar shaidar kamfani wato trademark.
Coca-Cola na neman kotu ta haramtawa Pop Cola, ma’aikatasu ko wakilansu amfani da alamar Pop Cola a duk wadansu abubuwa na talle kama daga kwalabe, robobi, motoci, takardu da sauransu har sai an kammala sauraron karar.
Tun da farko dai, lauyan Pop Cola, Offiong Offiong (SAN), ya baiyana cewa, wanda yake karewa ya kasha kudade masu yawa a harkar kasuwancinsa da tallata kayansa, inda ya kara da cewa lauyan Coca Cola ya gaza gabatar da kwararan hujjoji da zai kare bukarsa da su.
Offiong ya cigaba da cewa, korafin Coca Cola kan Pop Cola ba maganar kotu ba ce, kokawar neman nasara ce a kan kasuwanci.
Alkali Nasir Yunusa ya dage cigaba da sauraron karar har sai ranar 25 ga watan Afirilu na shekarar nan ta 2022.
(DAILY POST)