For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Kotu Ta Bayar Da Belin Ƴan Zanga-Zanga Kan Naira Miliyan 100, Ta Hana Su Ƙara Shiga Zanga-Zanga A Gaba

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba da beli na naira miliyan goma ga kowanne ɗaya daga cikin mutane goma da suka yi zanga-zangar #EndBadGovernance da ake zarginsu da yunƙurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu a tsakanin 1 ga Agusta zuwa 4 ga Agusta na wannan shekara.

Yayin yanke hukunci kan buƙatar belin, Mai shari’a Emeka Nwite ya ce dole ne masu neman belin su samar da masu tsaya musu, wadanda su zama masu mallakar kadarori a Abuja, tare da bayar da takardun kadarorin ga kotun.

Kotun ta kuma umarci waɗanda ake tuhuma da su samar da mutum guda a Abuja da zai tsaya musu tare da ajiye fasfo ɗinsu da hotuna guda uku da aka ɗauka kwanan nan a kotu.

Mai shari’a Nwite ya yi watsi da hujjojin da Sufeto-Janar na ƴansanda ya gabatar na ƙin amincewa da belin, sai dai ya umarci waɗanda ake tuhuma da kar su ƙara shiga wata zanga-zangar har sai an kammala shari’arsu.

Alƙalin ya kuma ba da umarnin a ci gaba da tsare waɗanda ake tuhuma a gidan yari har sai sun cika sharuddan belin na su.

Ana zargin wadanda ake tuhumar da laifin cin amanar ƙasa a yayin zanga-zangar da aka gudanar farkon watan Agusta a duk faɗin kasar, inda ake zargin sun yi yunƙurin yaƙar Najeriya.

Kotun ta sanya ranar 27 ga Satumba don cigaba da shari’ar.

Comments
Loading...