Kotun Daukaka Kara ta Abuja, ta dage sauraron karar da aka shigar ana bukatar a soke nasarar da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya samu a zaben 2019 a yau Laraba har sai 18 ga watan Mayu, 2022.
A baya ne dai, Amintattun Kungiyar Kula da Bibiyar Kundin Tsarin Mulki da Biyayya ga Doka, CSOCLC, ta shigar da daukaka kara tana kalubalantar gwamnatin Buhari, inda take bukatar a tsige shi a sanya tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar wanda ya zo na biyu a zaben Shugaban Kasa na 2019 a matsayin Shugaban Najeriya.
Kungiyar CSOCLC ta yi korafin cewa, bayanan da Buhari ya gabatar a babban zaben 2019 ba na gaskiya ba ne.
Alkalan Kotun guda uku wadanda Alkali Haruna Tsamani, a lokacin zaman na ranar Laraba, sun dage sauraron karar domin su bayar da dama ga gwamnatin Buhari ta shirya ta fitar da tsarin wakiltarta a shari’ar.
(SAHARA REPORTERS)