
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dakatar da bukatar Department of State Services (DSS) daga kama Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele kan zargin daukar nauyin ta’addanci da badakalar kudade.
Alkali J.T Tsoho, wanda ya dakatar da kamawar ya ce, DSS ba ta bayar da cikakkiyar shaidar da zata tabbatar da zargin da take na cewa Emefiele yana cikin harkokin daukar nauyin ta’addanci da badakalar kudade ba.
Akwai kuma rahotannin da ke nuna cewa, alkalin bai gamsu da bukatar ta DSS ba ne saboda rashin ganin amincewar shugaban kasa duba da girman matsalar da kuma tasirinta a kan tattalin arzikin Najeriya.
Haka kuma, a martanin DSS kan zanga-zangar da wasu gungun mutane suka yi suna kalubalantar karar da aka shigar da Gwamnan Babban Bankin Najeriyar, ta ce sa su aka yi.
Jami’an tsaron na sirri sun gargadi ‘yan Najeriya da su guji a yi amfani da su wajen ruguza tsarika, inda suka kara da cewa, aikinsu ba zai tsaya ba saboda masu kokarin amfani da farfaganda wajen hana binciken shari’a.
A wata sanarwar da DSS ta fitar ta bakin mai magana da yawunta, Peter Afunanya, ta tabbatar da cewa, tana nan a kan bakanta kuma ba zata yi rauni ba ko ta bayar da kai ga farfaganda ko cin mutunci ba.