Babbar Kotun Yanki da ke Gwagwalada a Abuja ta daure dalibi dan shekara 9, Hillary Yunana, a yau Alhamis saboda ya saci taliya da indomi a wani shago.
Mai laifin, wanda dan asalin kauyen Bassa ne da ke kan titin filin jirgin sama na Abuja, an tuhume shi da laifin fasa shago da kuma sata.
A hunkuncin da ya yanke, Alkalin Kotun Sani Umar, ya yankewa Yunana hukunci bayan Yunanan ya amsa laifinsa tare da neman afuwa.
Haka kuma, Alkali Sani ya baiwa mai laifin zabin biyan tarar naira 20,000 ko kuma zaman gidan yari na wata hudu.
Alkalin ya yi kira ga mai laifin da ya guji kara aikata laifin a gaba, sannan kuma ya baiyana cewa, ya yanke hukuncin ne domin tsoratar da duk masu yunkurin aikata irin wannan laifin a gaba.
Tun da farko dai, dansanda mai shigar da kara, Abdullahi Tanko, ya fadawa kotu cewa, mai laifin ya fasa tare da shiga shagon Gift Ugochukwu a ranar 4 ga watan nan na Maris.
Abdullahi Tanko ya ce, mai laifin ya saci ledar taliya guda 7 da ledar indomi guda 5 da kuma kudi naira 10,000, abubuwan da akai musu jimilla naira 13,000.
Ya kara da cewa, wannan laifi ne da ya saba da Sashi na 346 da na 287 na kundin Penal Code.
(NAN)