For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Kotu Ta Daure Matashi Shekaru 3 Bisa Laifin Satar Waya

Daga: Abdullahi Yawale

Babbar Kotun Shariar Musulunci mai lamba daya dake zamanta a Hadejia jihar Jigawa, ta daure wani matashi mai suna Babani Musa dan shekaru 30 zaman gida ajiya da gyaran hali na tsawon shekaru 3 bisa laifin satar wayoyin hannu.

Alkalin kotun Mai Sharia Yusuf Ibrahim Harbo, yace laifin da matashin ya aikata ya sabawa sashi na 180 da 144 na kundin Shariar Musulunci na jihar Jigawa.

Dan sanda mai gabatar da kara a kotun Sajent Abubakar Ubale yace ana tuhumar matashin ne da laifin satar wayoyin hannu guda biyu wadanda aka yi musu kiyasin kudi ₦8,500.

Tuni dai matashin ya amsa wadannan laifuka na shiga gida da kuma aikata sata.

Wannan dalili yasa kotun ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 3 a gidan ajiya da gyaran hali babu zabin biyan tara karkashin sashi na 145 da 186 na Kundin Shariar Musulunci na jihar Jigawa.

Comments
Loading...