For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Kotu Ta Daure ‘Yar Wasan Hausa, Sadiya Haruna Watanni 6 A Kurkuku

Kotun Majistare mai zama a Filin Jirgi na Malam Aminu Kano International Airport, a yau Litinin ta zartar da hukuncin dauri na watanni 6 ga jarumar wasan Hausa, Sadiya Haruna ba tare da zabin tara ba, saboda samunta da laifin cin zarafin abokin aikinta Isa A Isa.

An zargi jaruma Sadiya Haruna da cin zarafin Isa a faifan bidiyo wanda ta yada a shafukanta na sa da zumunta.

Lokacin da yake karanta hukuncin, Alkalin Kotun, Muntari Dandago ya ce, ya kama jarumar da laifi a kan duk zarge-zargen da akai mata.

A faifan bidiyon da jarumar ta yada, ta zargi jarumi Isa da yin luwadi, dan iska kuma manemin mata.

Sadiya Haruna ta yi zargin cewa, jarumin Isa ya nemi yin luwadi da ita a wani bidiyo da aka yada a Instagram.

Alkalin ya yanke hukuncin cewa idan har Sadiya Haruna ta cigaba da cin zarafin Isa to za ta fuskanci daurin shekaru 3 a kurkuku.

Alkalin ya ce, jarumar tana da watanni uku kafin ta rasa damar daukaka kara kan hukuncin.

Comments
Loading...