Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin dakatar da shugabancin jam’iyyar PDP na ƙasa daga rushe shugabannin jam’iyyar na Jihar Kano.
Alƙali Taiwo O. Taiwo a hukuncin da ya yi, ya gargaɗi PDP da cewar, ta bar shugabancinta na Jihar Kano daga matakin mazaɓu zuwa jiha su ci gaba da gudana har zuwa lokacin da za a yanke hukunci a kan ƙarar da aka shigar.
Jam’iyyar PDP a Jihar Kano na cikin tsaka mai wuya, musamman ganin shirye-shiryen fitar tsohon gwamnan jihar, Rabi’u Musa Kwankwaso daga jam’iyyar zuwa NNPP.
Kwankwaso dai shine jagoran jam’iyyar a jihar kuma ana ganin cewa shugabancin jam’iyyar na ƙarƙashinsa, abin da ya sa wasu ke neman da a rushe shi.
A kwanakin baya, TASKAR YANCI ta rawaito cewa wasu jiga-jigai a cikin tafiyar Kwankwasiya sun je wajen tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, inda suka baiyana cewa su ba zasu bi Kwankwaso zuwa NNPP ba, sannan suka buƙaci da a rushe shugabancin jam’iyyar na jihar wanda ke yiwa Kwankwaso biyayya.