Babbar Kotun Jihar Kano ta umarci tuɓaɓɓen Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero da ya dena kiran kansa a matsayin Sarkin Kano, sannan ta kuma umarci ƴansanda da su fitar da shi daga ƙaramar masarautar da ke kan titin State Road.
Kotun ƙarƙashin jagorancin Alƙaliya Amina Adamu Aliyu ta bayar da umarnin ne a yau Litinin, inda ta ce za a kasance a kan wannan hukunci da ta bayar har zuwa ranar 11 ga watan Yuni, 2024 lokacin da za a saurari cikakkiyar ƙarar.
Hukuncin kotun dai ya biyo bayan hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Kano na ranar Alhamis wanda ya dakatar da maganar dawo da Sarki Muhammadu Sunusi II a matsayin Sarkin Kano, ya kuma dakatar da dokar da rushe masarautun Jihar Kano biyar.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf dai ya musa hukuncin Babbar Kotun Tarayyar, inda yai zargin cewa, alƙalin da ake iƙirarin ya yanke hukuncin ba ya Najeriya, yana ƙasar Amurka lokacin da aka ce an yanke hukuncin, har ma ya ce zai miƙa maganar ga Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya, NGF.
Duk da wancan hukuncin dai, Sarki Sunusi II ya shiga fadar sarkin Kano a ranar Juma’a tare da fara aiki a matsayin sarki.