For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Kotu Ta Kama Babban Daraktan Yakin Neman Zaben Peter Obi Da Laifin Da EFCC Ke Zarginsa Da Shi

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta Abuja ta kama Babban Daraktan Yakin Neman Zaben Peter Obi, Doyin Okupe, saboda karya dokar Hukunta Masu Halatta Kudin Haramun.

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa, EFCC ce ta kama Okupe a shekarar 2019 kan zarge-zarge 59 da suka shafi halatta kudin haramun da karkatar da kudaden da yawansu ya kai naira miliyan 702.

An gurfanar da shi a gaban Alkaliya Ijeoma Ojukwu tare da wasu kamfanoni guda biyu da suka hada da Value Trust Investment Ltd da kuma Abrahams Telecoms Ltd.

An zargi Okupe da karbar kudade daga ofishin Mai Bayar da Shawara na Kasa a Kan Harkokin Tsaro, NSA, lokacin da Sambo Dasuki yana ofis.

Da yake karanta hukuncin a yau Litinin, Ojukwu, ya kama Okupe da laifin da ya saba da sashi na 16(1) da (2) na Dokar Hukunta Masu Halatta Kudin Haramun, ta hanyar karbar tsabar kudaden da suka haura ka’idar karbar kudade ba tare da an bi ta banki ba.

Alkalin ya ce, NSA ba banki ba ne, duk da tsohon shugaban kasa ya amince da kudaden, hakan ba ya nufin an amince da biyan kudin da ya saba da doka.

Alkalin ya ce, ya kama Dr. Doyin Okupe da laifi a tuhume-tuhume na 34, 35, 36 da kuma 59, yayin da kuma Okupe ya tsira daga tuhume-tuhume na 1 zuwa 33 bisa gazawar masu kara na shigar da kara na gurfanar da NSA a kan zargin karya Dokar Hukunta Masu Halatta Kudin Haramun.

Comments
Loading...