Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta rage tsayin shekarun da aka yankewa tsohon Dan Majalissar Wakilai, Farouk Lawan zuwa shekaru 5.
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ce ta yankewa Farouk hukunci a ranar 22 ga watan Yuni kan laifuffuka guda uku da suka hada da neman a bashi cin-hanci, yarda ya karbi cin-hanci da kuma karbar cin-hanci dala 500,000 daga sanannen dan kasuwar nan Femi Otedola.
Babbar Kotun Tarayyar ta yankewa Farouk hukuncin daurin shekaru bakwai-bakwai ga laifuka biyu na farko da kuma shekaru 5 ga laifi na uku.
Sai dai kuma a hukuncin da alkalai uku na kotun daukaka karar sukai ittifaki a kai yau Alhamis karkashin jagorancin Justice Monica Dongban Mensem, kotun ta kwashe hukunci na farko da na biyu.
Kotun ta amince cewar, hukuncin da aka yanke kan neman cin-hanci da yarda domin karbar cin-hancin dala miliyan 300 daga wajen Otedola a matsayin wadanda ba a sami madogara ba.
Kotun daukaka karar ta gano cewar a hukuncin farko da aka yankewa Farouk Lawan an iya tabbatar da laifi na uku ne kadai wanda shine karbar cin-hanci na dala 500,000 daga Otedola.
Da take yanke hukunci, kotun daukaka karar ta tabbatarwa Farouk hukunci na uku wanda a shi aka yanke masa hukuncin daurin shekaru biyar.
Farouk Lawan ne dai ya shigar da karar, yana kalubalantar hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja wadda tai masa hukuncin baya.
(THE NATION)