Daga: DW Hausa
Kotun koli a Iraki ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya kan mutumin da ya kashe wasu ‘yan jarida biyu da suka yi zanga-zangar kin jinin gwamnati a birnin Basra a 2020.
Mutumin da aka yanke wa hukuncin, wanda aka bayyana sunansa da “H.K” ya amsa dukkannin laifuffukan da kotun ta tuhume shi da aikatawa, mutumin da aka kama a farkon shekarar 2021 tare da wasu mutane hudu, bai danganta kansa da wata kungiya ta ‘yan tada kayar baya ba.
Ahmad Abdessamad mai shekaru 37 wakilin gidan Talabijin na Al-Dijla da mai daukar hotonsa Safaa Ghali mai shekaru 26, sun mutu ne yayin da ‘yan bindiga suka bude musu wuta a cikin wata mota yayin da suke tuki a garinsu na Basra a watan Janairun 2020.