A yau Talata wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja, ta soke korar da aka yiwa tsohon Sarkin Kano Sunusi Lamido Sunusi daga Kano bayan tube shi daga sarautar Kano.
Kotun ta yi wannan hukuncin ne a yau Talata, bayan ta bayyana abin da akaiwa sarkin a matsayin abin da ya saba doka da kuma tauye hakkinsa na dan’adam.
Da yake gabatar da hukuncin, Alkali Anwuli Chikere, ya bayyana yanda aka tilasta fitar Sarki Sunusi daga fadar Kano a watan Maris na shekarar 2020 bayan tube shi tare da kai shi jihar Nasarawa ba tare da amincewarsa ba a matsayin cin zarafin ‘yancinsa na gudanar da rayuwa da kuma zirga-zirga.
Alkalin ya kalubalanci dokar da gwamnatin Kano tai amfani da ita wadda aka kirkira shekarar 2019 a matsayin dokar da ta saba da ‘yancin dan’adam.
Ya kuma bayyana cewa, Sunusi na da damar zama a kowanne bangare na Najeriya gwargwadon bukatarsa.
Alkali Chikere ya ci tarar gwamnatin Kano, hukumar ‘yan sanda ta kasa da kuma hukumar tsaro ta farin kaya Naira Miliyan 10 a matsayin hukuncin cin zarafin da akaiwa tsohon sarkin.
Sannan kuma ya umarce su da su sanar da bayar da hakurinsu ga tsohon sarkin a akalla jaridu biyu na Najeriya.
Alkalin ya kuma tsame babban lauyan Najeriya, Abubakar Malami daga karar, inda ya ce sarkin ya gaza gabatar da hujjojin tuhumar lauyan.