For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Kotu Ta Soke Zaben APC Na Fidda Gwani Na Gwamna A Akwa Ibom

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Uyo, ta soke takarar Akan Udofia a matsayin mai yi wa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) takarar gwamna a Jihar Akwa Ibom a zaben shekarar 2023.

Kotun ta bayyana cewa, Akan Udofia bai taba zama dan jam’iyyar APC ba.

A hukuncin da ta yanke a jiya Litinin, Alkaliya Agatha Okeke ta yi umarnin a sake sabon zaben fidda gwani cikin kwanaki 14 daga jiya da aka yanke hukunci.

Hukuncin kuma ya hana Akan Udofia shiga sabon zaben fidda gwanin.

Tsohon Mai Temakawa Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari a kan Harkokin Yankin Niger Delta, Ita Enang ne ya shigar da karar, yana kalubalantar takarar Udofia.

Enang ya yi zargin cewa, Udofia ba dan jam’iyyar APC ba ne a lokacin da aka gudanar da zaben fidda gwanin, inda ya bayyana cewa, Udofia ya yi takara a zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP wanda aka gudanar a ranar 25 ga watan Mayu kafin ya zo ya yi a APC a zaben fidda gwanin da aka gabatar a ranar 26 ga watan na Mayu.

Comments
Loading...