For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwani Na APC A Taraba

Alkali Obiora Egwatu na Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta soke zaben fidda gwani na gwamna a jam’iyyar APC wanda ya baiwa Sanata Emmanuel Bwacha nasara a matsayin dan takarar APC na gwamna a Jihar Taraba a zaben 2023.

Da yake yanke hukunci, Alkali Egwuatu ya bayyana cewa, duba da hujjojin da aka gabatar a gabansa daka dukkanin bangarori, zaben fidda gwanin da APC ta gabatar a ranar 26 ga watan Mayun wannan shekarar, wanda aka sanar da Bwacha a matsayin dan takarar gwamna a zaben shekarar 2023, sokakke ne.

Hukuncin dai ya biyo bayan korafin da sanata mai wakiltar Taraba Central, Yusuf Yusuf ya gabatar.

A watan da ya gabata ma, wata Babbar Kotun Tarayya da ke Jalingo ta soke takarar Bwacha a wani hukuncin na daban wanda wani mai neman takarar gwamnan da ake kira David Kente ya shigar.

A duk hukuncin guda biyu, kotunan biyu, sun bukaci shugabancin jam’iyyar APC da ya gudanar da sabon zaben fidda gwani a jihar.

Comments
Loading...