For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Kotu Ta Ƙwace Kujerun Ƴan Majalissa 20 Saboda Sauya Sheƙa Zuwa APC

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta kori ƴan majalissar Jihar Cross River guda 20 waɗanda suka fice daga jam’iyyar PDP suka koma jam’iyyar APC.

A lokacin da yake yanke hukunci kan karar da aka shigar kan ‘yan majalissar, Alƙali Taiwo Taiwo, a jiya Litinin ya ce, kotun ta yanke cewar ƴan majalissar zasu bar kujerunsu ne tun da sun yi watsi da jam’iyyar da ta yi sanadiyyar cin zaɓensu.

Hukuncin ya biyo bayan ƙarar da jam’iyyar PDP ta shigar mai lamba FHC/ABJ/CS/975/2021.

Alƙali Taiwo ya yi watsi da neman lauyan wadanda ake tuhuma na cewa, PDP ba ta ikon shigar da ƙara kan lamarin.

Alƙali Taiwo ya yanke hukuncin cewa, iƙirarin ƴan majalissar na cewa akwai ɓaraka a jam’iyyar PDP a matsayin dalilin da ya tilasta su barin jam’iyyar, a matsayin ƙoƙarin kawar da hankalin kotu.

Alƙalin, wanda ya amince da dukkanin abin da PDP ta nema ya baiyana cewa, abin takaici ne cewar ƴan siyasa a ƙasar nan, suna ɗaukar ƴan ƙasa a matsayin marassa muhimmanci da zarar sun ci zaɓe.

Ya baiyana cewa, ba zai yiwu a cigaba da kasancewa a cikin aikata laifi, sannan a yi tsammanin wani abun alkhairi zai faru ba.

(PUNCH).

Comments
Loading...