Kotun Ƙoli ta tabbatar da ƴancin ɗalibai Musulmai mata a jihar Lagos na sanya hijabi a makarantu ba tare da tsangwama ko cin mutumci ba.
A hukuncin da mafiya rinjaye na alƙalan kotun ƙolin suka yi a yau Juma’a a Abuja, sun amince da sanya hijabin a makarantun.
Alƙalan sune Alƙali Olukayode Ariwoola, Alƙaliya Kudirat Kekere-Ekun, Alƙali John Iyang Okoro, Alƙaliya Uwani Aji, Alƙali Mohammed Garba, Alƙali Tijjani Abubakar da kuma Alƙali Emmanuel Agim.
Shida daga cikin alƙalan sun yi hukuncin amincewa da sanya hijabin, yayin da alƙali guda ya ƙi amincewa.
A dai watan Fabarairu na shekarar 2017 ne Gwamnatin Jihar Lagos ta je Kotun Ƙoli domin ƙalubalantar hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara na ranar 21 ga watan Yuli na shekarar 2016 wanda ya dawo da sanya hijabi ga dalibai mata a makarantun gwamnati na Jihar Lagos.
Wannan kuwa ya faru ne, bayan gwamnatin jihar ta yi ƙoƙarin neman tabbatar da hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yankin Lagos amma abun ya ci tura.