Kutun Daukaka Kara da ke Kano, ta kori karar da Malam Aminu Ibrahim Ringim ya shigar yana kalubalantar zaben shugabannin jam’iyyar PDP reshen jihar Jigawa.
Tun bayan faduwa zaben gwamnan da Aminu Ibrahim Ringim yai a shekarar 2019 ake samun sa’insa tsakaninsa da tsohon ubangidansa, Sule Lamido a jam’iyyar PDP.
Malam Aminu Ringim da magoya bayansa na zargin bangaren Sule Lamido da yin danniya da kuma yunkurin dora musu wanda ba sa so a jam’iyyar.
Bayan kammala zaben shugabannin jam’iyyar PDP a jihar Jigawa, Malam Aminu Ringim ya shigar da kara, inda yake kalubalantar ingancin zaben wanda mutanen Sule Lamido suka zama shugabannin jam’iyyar a jihar sanadiyyarsa.
Malam Aminu Ringim yana zargin cewa ko zaben shugabannin a matakin mazabu ba ai ba, amma aka gudanar da zaben a matakin jiha, wannan ta sa ya garzaya babbar kotu a jihar Jigawa domin neman adalci.
KU KARANTA: Ziyarar Kwamatin Takarar Shugaban Kasar Atiku Jihar Jigawa, Ta Banbance Tsakanin Tsaki Da Tsakuwa
Babbar Kotun ta kori karar ne saboda rashin ikon saurarar karar da take da ita a cewarta, inda ta nuna cewa, rigimar jam’iyya ce kuma a koma jam’iyyar domin a magance ta.
Bayan wannan hukunci ne, Malam Aminu Ringim ya daukaka kara a kotun daukaka kara da ke Kano, yana neman kotun da ta soke hukuncin babbar kotun jihar Jigawa.
Sai dai kuma, a yau 14 ga Janairu na wannan shekara ta 2022, alkalin kotun ya bayyana cewa hukuncin Babbar Kotun da ya gabata shine dai hukunci har yanzu, inda yai watsi da karar.
Alkalin Kotun Daukaka karar ya karanta hukuncin kamar haka: “A yau, 14 ga Janairu, 2022. Kotun Daukaka Kara ta Kano Banagaren Yanke Hukunci, ya yanke hukunci kan karar da Alhaji Muktar Ibrahim Gagarawa da wasu su 2 (a matsayin jagororin tsagin jam’iyyar PDP bangaren Malam Aminu Ibrahim Ringim reshen jihar Jigawa) inda suke karar PDP da wasu mutane 6.
“Kotun a hukuncin da ta yanke, ta tabbatar da hukuncin Babbar Kotun Jihar Jigawa wanda Alkali Hon. Justice Musa Ubale ya yi na cewar karar da aka shigar ta shafi rikicin cikin gida ne na jam’iyya wanda ba na shari’a ba, saboda haka kotu ba ta hurumin saurarar karar.
“Saboda haka kotun daukaka kara ta kori wannan daukaka karar haka kuma tana umartar da a biya jam’iyyar wadanda aka shigar da karar (PDP da sauran su) tara N500,000.00.” in ji alkalin.