For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Kotun Koli Ta Kori Karar Da Shugaba Buhari Ya Shigar Kan Dokar Zabe

Kotun Koli ta yi watsi da karar da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami wadda suka shigar suna bukatar fassarar Sashi na 84(12) na Dokar Zabe ta 2022.

Alkalan kotun su bakwai karkashin Alakali Musa Dattijo Muhammad a yau Juma’a sun hadu wajen amincewa da cewa karar ta saba ka’idojin kotu.

A lokacin karanta hukuncin kotun wanda Alkali Akomaye Agi ya yi, Kotun Kolin ta ce, tun da Shugaba Buhari a farko ya amince da Sashi na 84(12) na Dokar Zabe ta 2022, to ba shi da damar neman a goge sashin.

“Babu wani tanadi na kundin tsarin mulki da ya baiwa Shugaban Kasa damar kalubalantar ingancin wata doka wadda ya sanyawa hannu ko kuma yaki sanyawa hannu. A wannan dokar kuma, Shugaban Kasar ya sanyawa dokar hannu,” in ji shi.

“Shugaban Kasa ba shi da karfin nema ko tilastawa Majalissar Tarayya domin ta canja wani bangare na dokar da yi wadda shi ma ya kasance cikin yin tarayya da ita a lokacin yin.”

Agim ya kuma ce, “Wannan kara ba zata samu karbuwa ba a wannan kotu saboda abin da ke cikin Sashi na 1(1) (a) na dokar Additional Jurisdiction of the Supreme Court Act.”

An dai shigar da karar ne biyo bayan hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Umuahia a Jihar Abia wadda ta soke Sashi na 84(12) saboda ta saba da tanade-tanaden da ke cikin Kundin Tsarin Mulki na 1999 da ke sassa 66(1)(f), 107(1)(f), 137(1)(f) da kuma na 182(1)(f).

Comments
Loading...