A yau Juma’a ne Kotun Koli ta baiyana cewa, ‘Executive Order 10’ kan biyan kudaden bangaren Shari’a na Jihohi da Majalissun Dokoki a matsayin haramtacciya wadda ta sabawa kundin tsarin mulki.
Mafi yawan alkalan kotun da suka zauna sun amince da cewa, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya haura ka’idar da Kundin Tsarin Mulki ya ba shi wajen sanya EO 10.
Alkalai shida cikin bakwai ne suka tabbatar da haramta EO 10 a zaman kotun na yau.
Haka kuma kotun kolin ta kori karar da gwamnoni suka shigar suna kalubalantar gwamnatin tarayya kan kudade kimanin naira biliyan 66.