For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Kotun Ƙoli Ta Sanya Ranar Sauraron Ɗaukaka Ƙara Kan Zaɓen Kano

Kotun Ƙolin Najeriya ta sanya ranar Alhamis 21 ga watan Disambar nan domin fara sauraron ɗaukaka ƙarar da aka yi kan zaɓen gwamnan Jihar Kano wadda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya shigar.

Wannan rana na ɗauke ne a sanarwar da kotun ta aike wa dukkan ɓangarorin da ke ciki ƙarar.

Idan ba a manta ba, Kotun Ɗaukaka Ƙara a ranar 17 ga watan Nuwamba, a hukuncin da alƙalai uku na kotun su kai tarayya a kai, sun ƙara karɓe nasarar Gwamnan Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP tare da ƙara bayyana Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashen zaɓen ranar 18 ga watan Maris na Jihar Kano.

Kotun Ɗaukaka Ƙarar dai ta kori ɗaukaka ƙarar da Gwamna Yusuf yai ta hanyar la’akari da matsayinsa na kasancewa ɗan jam’iyyar NNPP, inda ta bayyana cewar Gwamnan bai shiga NNPP ba kafin lokacin zaɓen fidda gwani.

Sai dai kuma wata rikita-rikitar ta ɓarke bayan da takardun hukuncin kotun sun bayyana inda suka nuna cewar kotun Gwamna Abba Kabir Yusuf ta bai wa nasara.

Daga bisani kotun ta ce an samu kura-kuran rubutu ne a takardun hukuncin, abin da ya sa ta buƙaci ɓangarorin da ke cikin shari’ar su dawo da takardun domin yin gyara, sai dai kuma ɓangaren Gwamna Abba ba su amince da hakan ba.

Comments
Loading...