Gwamnatin jihar Yobe ta bukaci iyaye da su bar ‘ya’yansu mata su shiga aikin sojan Najeriya domin su taimaka wajen kare martabar yankunan kasar.
Mai bawa Gwamna Mai Mala Buni shawara na musamman kan harkokin tsaro da shugaban kwamitin daukar ma’aikata na jihar Yobe, Brig. Janar Dahiru Abdulsalam (rtd) ya bayar da wannan umarni ne a lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a runduna ta 241 Recce Battalion Nguru, wurin da ake gudanar da aikin tantance ma’aikata 82 na yau da kullum na jihar.
KU KARANTA: An Saki Sunayen Wadanda Suka Sami Aikin ‘Yan Sanda
Ya ce yana da kyau ‘yan jarida da sauran masu ruwa da tsaki su wayar da kan iyaye a fadin kananan hukumomin jihar 17 da su karfafawa ‘ya’yansu mata da su shiga aikin soja.
Sai dai yace yana da matukar wahala mata daga wannan yanki na kasar su shiga aikin soja, saboda addini da al’adu.
Daga: Muhammad Sulieman Yobe