For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Ku Dena Yaudarar ‘Yan Najeriya – Falana Ga Gwamnatin Tarayya

Sananne Babban Lauyan Najeriya, Femi Falana ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta dena yaudarar ‘yan Najeriya game da batun masu daukar nauyin ta’addanci a kasar.

Babban Lauyan ya baiyana hakan ne a tattaunawar sa da jaridar PUNCH bayan bayanan Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Muhammed na cewa Gwamnatin Tarayya ta bankado mutane 96 da ke daukar nauyin ta’addanci a kasar.

Falana ya ce, abin kaico ne cewa, Gwamnatin Tarayya wadda take nuni da tana kokari wajen magance ta’addanci da cin hanci da rashawa a ce tana kare masu daukar nauyin ta’addanci daga fuskantar hukunci.

Babban Lauyan ya ce, “Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya (Abubakar Malami) a bara ya ce sun gano mutane 400 da ke daukar nauyin ta’addanci. Yanzu kuma Lai Muhammed ya ce sun gano mutane 96 a dai wannan shekarar. Ko dai adadin na nufin 496? Ya kamata su dena yaudarar ‘yan Najeriya.”

A shekarar baran dai Malami ya ce yajin aikin da bangaren shari’a suke yi ne ke jawo tsaiko wajen gurfanar da wadanda aka gano, amma Falana ya ce, yanzu kimanin watanni 8 da janye yajin aikin amma Malami ya kasa kama masu daukar nauyin ta’addancin.

“Babban Lauyan Gwamnatin ya ce yajin aikin da ma’aikatan kotuna ke yi ne ya jawo tsaiko wajen gurfanar da masu daukar nauyin ta’addancin. An janye yajin aikin sama da watanni 8 da suka wuce. Yanzu kuma me ye uzurinsu?” In ji Falana.

Comments
Loading...