For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Ku Fallasa ‘Yan Takara Masu Takardun Bogi – INEC Ga Masu Zabe

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, INEC, a ranar Laraba ta sanar da masu zabe da su shigar da duk dan takarar da ya gabatar da takardun da suka tabbatar da na bogi ne yayin da yake neman takara.

Kwamishinan Kasa na Hukumar INEC kuma Shugaban Kwamitin Yada Labarai da Wayar da Kan Masu Zabe na Hukumar, Festus Okoye ne ya yi wannan kiran a Abuja.

Kiran ya zo ne a lokacin da Hukumar ta baiyana bayanan ‘yan takarar da ke son tsayawa takarar gwamnan Ekiti wanda za a gudanar ranar 18 ga watan Yuni.

Okoye ya kuma sanar da cewa jerin bayanai da takardun ‘yan takarar an kakkafa su a ofishin INEC na jihar da kuma na kananan hukumomin jihar.

Ya ce, baiyana bayanan ya zo dai-dai da tanadin doka a sashi na 31(3) na Dokar Zabe ta shekarar 2010 (wanda akaiwa kwaskwarima), wanda yai tanadin cewa, dole ne Hukumar ta wallafa takardun dan takara cikin kwanaki 7 da karbar takardun a guraren da yake nufin yin takara.

“Haka kuma, kamar yanda yake a sashi na 31(4) na Dokar Zabe, duk wani wanda yake da hujjoji gamsassu ya kuma san cewa takardun da wani dan takara ya gabatar tare da takardar neman takararsa na bogi ne, zai iya shigar da kara Babbar Kotun Tarayya, Babbar Kotun Jiha, ko ta Abuja yana kalubalantar wannan dan takara.

“Muna kira ga al’umma da su shiga harkar inganta zabubbuka ta hanyar bincikar takardun da ‘yan takara ke gabatarwa . . .”.

Comments
Loading...