For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Ku Manta Da Peter Obi, Tinubu Ba Zai Janye Daga Takara Ba Saboda Rashin Lafiya – Keyamo

Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaba na Jam’iyyar APC ya ce, dan takarar jam’iyyar, Bola Ahmed Tinubu ba zai janye daga shiga zaben shekarar 2023 ba saboda matsalar rashin lafiya kamar yanda magoya bayan dan takarar jam’iyyar LP, Peter Obi suke yadawa a kafafen sa da zumunta.

Kwamitin ya kuma bukaci Peter Obi da ya janye daga takarar idan har ba shi da abun da zai fadawa ‘yan Najeriya.

A wani faifan bidiyo da akai ta yadawa dai, Obi ya zargi wasu ‘yan APC masu tallata Tinubu na gargadin Yarabawa da kar su zabi Peter Obi domin idan sun zabeshi kamar sun zabi a yi tashar jirgin ruwa a Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas.

Amma da yake mayar da martani a yau Litinin, Daraktan Kafafen Yada Labari da Hulda da Jama’a kuma Mai Magana da Yawun Dan Takarar Shugaban Kasa na APC, Festus Keyamo ya ce, “Zamu Kalubalanci Mr. Peter Obi da ya bayyana inda ya jiyo da kuma sunayen wadanda suke da alhakin kirkirar wannan sakon WhatSapp na karya.

“Muna son mu bayyana cewa, a bayyane yake Mr. Peter Obi da gangan ya kirkiri sakon ya watsa wannan bidiyon na cin zarafi da kan sa a matsayin hanyar yakin neman zabe, don a tausaya masa saboda sukarsa da za ai da bangaranci, bayan a gaskiyar magana, shine wanda yake rura wutar bangaranci.

“Muna kuma so mu yi amfani da wannan dama, mu karyata labaran karya masu yaudararwa da ke kan shafukan magoya bayan Mr. Peter Obi na cewa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai janye daga takara saboda matsalar rashin lafiya”.

Comments
Loading...