Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari a jiya Asabar ya yi allawadai da harin da aka kaiwa waɗanda ba ƴan ƙasa ba da kuma jami’an tsaro a yankin Kudu maso Gabas, inda yai kira ga ƴan ƙasa da su tona asirin waɗanda suka kai harin domin su fuskanci hukunci.
A jawabin da Babban Mai Temaka masa a Kan Kafafen Yaɗa Labarai, Malam Garba Shehu ya sanyawa hannu, Shugaban Ƙasar na mayar da martani ne kan yankan ragon da aka yiwa wasu ƴan Nijar 6 da kuma kisan wulakancin da aka yiwa wasu jami’an ƴansanda suna tsaka da aikinsu.
Shugaban Ƙasar ya kuma yi kira ga al’umma da shugabannin addinai da su tashi tsaye wajen yin tur da kisan tare da kare martabar al’adu da addinin da aka gada.
Buhari ya kuma yi alƙawarin cewa, gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa wajen gaggauta bincike da kuma gurfanar da waɗanda suka kitsa kisan gillar.
Ya ƙara da cewa, gwamnatin tasa a shirye take wajen ganin ta dawo da tsaro a yankin Kudu maso Gabas da ma sauran sassan Najeriya, inda ya ce samun rahotannin kashe-kashe a ko’ina a ƙasar nan abun takaici ne da kuma allawadai.
A ƙarshe, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan jami’an tsaron da suka rasa rayukansu da kuma iyalan ƴan ƙasar Nijar ɗin da su ma aka yiwa kisan gillar.