Kudirin Kasafin Kudin jihar Jigawa na shekarar 2022 ya tsallake karatu na biyu a majalissar dokokin jihar a yau Alhamis.
Wakilin JTV, Ibrahim Isyaku wanda ya halarci zaman majalissar, ya bayyana cewa, shugaban masu rinjaye na majalissar, Habu Maigatari ne ya gabatar da kudirin ga majalissar, inda wakili mai wakiltar mazabar Ringim, Aminu Sankara ya goyi bayansa.
Ya bayyana cewa, ya zama wajibi su bar gwamnati ta cigaba da aiyukan cigaban da take yi a fadin jihar.
Wakilai da suka hada da Aliyu Ahmed mai wakiltar Kirikasamma, Haruna Aliyu mai wakiltar Miga da Sani Saleh mai wakiltar Kaugama sun yi sharhi kan nuna goyon bayan duba kudirin a karatu na biyu.
Sun bayyana cewa, kasafin ya zo a lokacin da ya dace ta yanda zai inganta walwala da jin dadin al’ummar jihar Jigawa.
Kakakin majalissar, Idris Garba Jahun, ya mika daftarin kudirin ga kwamitin kasafin kudi na majalissar domin dubawa da kuma kawo rahoto a kai cikin sati biyu.
Gwamna Muhammad Badaru Abubakar na jihar Jigawa ne ya gabatar da Kudirin a jiya Laraba ga majalisar, inda ya bayyana cewa jihar za ta kashe Naira Biliyan Dari da Saba’in da Bakwai da Miliyan Dari Bakwai da Saba’in da Tara da Dubu Dari Biyar da Tamanin da Takwas (177, 795,588) a shekarar 2022 domin yin aiyuka da gudanar da gwamnati.
Majalissar ta dage zamanta har zuwa ranar Talata 22 ga watan Disamba na wannan shekarar.