For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Kungiyar CAN Ta Yi Barazanar Daukar Mataki Idan A Kai ‘Yan Takara Musulmi A Najeriya

Kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN, ta yi gargadin cewa ba za su goyi bayan dan takara Musulmi mataimaki Musulmi ba a zaben shekarar 2023.

Kungiyar ta ce yin hakan zai iya jawowa rushewar Najeriya.

Babban Daraktan Gungun Magoya Bayan Tinubu (Tinubu Support Group), Abdulmumini Jibrin, a ranar Litinin ya bayyana cewa ba zai zama matsala ba don Tinubu ya zabi mataimaki Musulmi a takararsa.

Ya kara da cewa ‘yan Najeriya za su zabi cancanta ne ba wai bangaranci ko addini ba.

Abdulmumini ya bayyana cewa, yanzu haka a Majalissar Wakilai ta Tarayya, Kakakin Majalissar, Femi Gbajabiamila da Mataimakin Kakakin Majalissar Idris Wase duk Musulmai ne.

Ya kara da cewa a Majalissar Dattawa ta 6 da 7, shugaban majalissar David Mark da mataimakin shugaban majalissar Ike Ekweremadu dukkaninsu Kiristoci ne.

A littafin da ya kaddamar kwanannan, tsohon jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bisi Akande, ya bayyana cewa, an yi yunkurin Tinubu ya zama mataimakin Buhari a shekarar 2015, haka ma a shekarar 2007 ya zama mataimakin Atiku, amma dukkanninsu sun kasance Musulmi.

Akande ya bayyana cewa, mutanen yankin Kudu maso Yamma ba sa la’akari da addini lokacin yin hukunci a zabe.

Da yake magana da PUNCH a ranar Talata, mai magana da yawun Shugaban Kungiyar Kiristocin Najeriya, Rev. Bayo Oladeji ya bayyana cewa kungiyar CAN ba za ta goyi bayan ba ko da Kiristoci ne biyu suka fito neman takarar a matsayin shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa a zaben 2023.

Ya bayyana cewa, abin da ya faru a ranar 12 ga Yuni na 1993, inda MKO Abiola tare da Babagana Kingibe suka tsaya a takara a matsayin shugaban kasa da mataimaki, ba zai yiwu ba a shekarar 2023.

Oladeji ya ce, “’yan siyasa za su iya maganar siyasarsu, amma mu dai mun bayyana matsayarmu. Duk jam’iyyar da ta ce za ta tsayar da iya Musulmai ko Kiristoci to za ta fadi.

“Yanzu ba shekarar 1993 ba ce, a inda ma ake samun ‘yan takara Musulmi da Kiristan ma coci-coci suna fama, Allah kadai ya san yawan Kiristocin da aka kashe.

“Ka yi tunanin yanda abin zai kasance idan muka sami Musulmi biyu a kan mulki. Kundin Tsarin Mulki ya ba da damar samar da daidaito tsakanin addinai. Saboda haka idan suna son tsayar da Musulmi da Musulmi su tsayar. Amma mu ba za mu goyi bayan wadanda ba sa mutunta mutane ba. Ku kyale kowacce jam’iyya ko gwamnati ta gwada, za su san cewa Kiristoci ba kanwar lasa ba ne a Najeriya.

“Najeriyar nan ta dukkaninmu ce. Saboda haka idan suka gwada za su gani. Wadanda suke kokarin kawo Musulmi da Musulmi su binciki me ya faru da takarar MKO Abiola da Kingibe. Idan har sukai Musulmi da Musulmi a wanna karon, abin da zai biyo baya ba zai zama mai dadi ba.”

Daga: PUNCH

Comments
Loading...