Kungiyar Daliban Najeriya ta Kasa, NANS ta yi allawadai da matakin Kungiyar Malaman Jami’o’i, ASUU, na shiga yajin aikin makonni hudu a yau Litinin domin nunawa Gwamnatin Tarayya bacin ransu.
Kungiyar ta yi alkawarin aiwatar da abubuwa da suka hada zanga-zanga domin tabbatar da cewa an dage yajin aikin, malamai da dalibai sun koma ajuzuwa.
Da yake magana da jaridar PREMIUM TIMES a yau Litinin, Shugaban NANS, Asefon Sunday ya yi korafin cewa, daliban Najeriya a ko da yaushe su ke shiga halin ni ‘ya su idan aka samu sabani tsakanin gwamnati da ASUU.
Asefon ya ce, “Ba ma goyon bayan ASUU, ba ma goyon bayan gwamnatin tarayya. Kuma duk abin da za mu yi domin tabbatar da mun dawo ajuzuwa shine abun da za mu yi. Kuma ina tabbatar muku cewa a cikin awanni 24 masu zuwa za ku ga abubuwan da za su faru a kasar nan.”
Kungiyar ta ce, radadin yajin aikin watanni tara da akai a baya wanda aka dakatar a watan Disamba na 2020 har yanzu bai bar jikin daliban ba.
“Duk lokacin da giwaye biyu suke fada da juna, ciyawa ce take shan wahala. Daliban Najeriya ko yaushe sune suke shan wahala a karshe. Mu muke shan wahala,” in ji shugaban na NANS.