For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Kungiyar Dalibai ta Kasa ta Gargadi Gwamnatin Tarayya kan Cire Tallafin Mai

Kungiyar Daliban Najeriya ta Kasa, NANS, ta gargadi Gwamnatin Tarayya da kar ta aiwatar da shirinta na cire tallafin mai tare da kara kudin albarkatun mai a kasar.

A jawabin da kungiyar ta saki jiya Juma’a, daga shugabanta na Zone D, Comrade Fiyinfoluwa Tegbe tare Jami’in Hulda da Jama’a, Comrade Emmanuel Esiegbe, duk sun bayyana cewa, kungiyar za ta dau tsattsauran mataki wajen bijirewa cire tallafin, inda suka kara da cewa, cire tallafin ba komai zai jawo ba sai kara jefa tallakawan Najeriya cikin kunci.

 A shirye-shiryenta na kalubalantar cire tallafin, kungiyar ta ce, an shirya zaman gaggawa na ‘yan-majalissar dattawa na kungiyar yankin Kudu maso Yamma domin a jawo hankalin masu ruwa da tsaki, da shugabanni da sauran mutane kan kalubalen, inda ta kara jaddada cewa nade hannu yayin da matsala ke tunkarowa zai jawo matukar koma baya ga bangaren dalibai.

 A jawabin kungiyar mai taken: ‘Tsadar Farashin Mai: Tabon da Muke Gwagwarmayar Iya Jurewa’, ta ce, maimakon gwamnati ta cika alkawuran da tai na ragewa mutane matsalolinsu, kara jefasu ciki take yi, inda ta kara da cewa, lokaci ya yi da daliban Najeriya za su nemawa kansu mafita ta hanyar bijirewa duk wani tsarin gwamnati na rashin adalci.

Jawabin yana cewa: “ba karamin abin kaico ba ne, gwamnatin da muka baiwa damar mulkarmu domin ta saka mana da samar da tsaro da walwala ta zama abin kaico, ta fi sha’awar ta kara jefa mutane cikin matsanancin yanayi.”

“Fatanmu ne gwamnatin tarayya karkashin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ta saurari dalilanmu da ajjiye maganar cire tallafin mai, haka kuma, mun shirya tsaf mu bijirewa tsarin rashin adalci ba kawai a matsayin daliban Najeriya ba, a a, har ma dukkan mutanen kasar.”

Comments
Loading...