Kungiyar ‘Yan awaren IPOB a Najeriya ta bukaci mazauna Jihar Anambra da su fito domin kada kuri’ar su a zaben gwamnan da zai gudana gobe Asabar, wanda a baya tace ba zata bari ayi ba har sai an saki shugabanta Nnamdi Kanu dake tsare.
Mai magana da yawun kungiyar Emma Powerful, ya gabatar da sabuwar sanarwar da ta dage zaman gida na mako guda da suka saka, yayin da suka yi gargadi dangane da duk wani yunkuri na gudanar da magudi lokacin zaben.
Sanarwar ta godewa magoya bayan kungiyar dake ciki da wajen Najeriya dangane da fafutukar da suke yi na abinda suka kira ‘yantar da mutanen yankin su.
Kungiyar ta yi gargadin cewar kada masu adawa da fafutukarsu su yi mummunar fassara dangane da matakin da suka dauka, yayin da suka ja kunne dangane da daukar matakin tirsasawa jama’ar yankin.
A karshe kungiyar IPOB ta bayyana fatar ganin dattawan su da shugabannin addini da na siyasa da kuma masu ruwa da tsaki sun cika alkawarin da suka musu na ganin an sako shugaban su Nnamdi Kanu.
Rundunar Yan Sandan Najeriya tace ta shirya tsaf domin tabbatar da tsaro lokacin zaben, yayin da Sufeto Janar Usman Baba yace sun tura jami’an Yan Sanda dubu 34 domin kare lafiyar jama’a da malaman zabe.
Hukumar zaben kasar ta hannun shugaban ta Farfesa Mahmood Yakubu ta bayyana kammala shirye shiryen gudanar da zaben wanda zai gudana gobe asabar.
Jam’iyyu 18 suka shiga takarar gwamnan Anambra, yayin da wakilan su suka sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya lokacin bikin da tsohon shugaban kasa Abdusalami Abubakar ya jagoran ta.