Hadaddiyar Kungiyar Kwadago ta Najeriya ta janye zanga-zangar da ta shirya a fadin kasar nan a ranakun 27 ga Janairu da 2 ga Fabarairu na 2022.
Kungiyar ta dau wannan mataki ne a zaman Shugabanninta na Kasa wanda akai ta yanar gizo a yau Talata.
Shugaban Kungiyar Kwadagon, Ayuba Wabba, wanda ya sanar da labarin a ganawarsa da ‘yan-jaridu ya ce, an dau matakin ne saboda janye yunkurin Gwamnatin Tarayya na cire tallafin mai.
Ya ce, ‘yan-kungiyar NLC wadanda aka umarta da su fito zanga-zangar, za sanar da su cewa an fasa gudanar da zanga-zangar biyo bayan hukuncin fasa cire tallafin.
Ayuba Wabba ya ce, “Bayan matsawar kungiyar kwadago wajen kiran ‘yan Najeriya da sauran kungiyoyin cigaban al’umma, da su fito zanga-zangar nuna kin amincewa da cire tallafin mai, Ministar Kudi a ranar 24 ga Janairu ta sanar da fasa shirin kara farashin mai.
“Matsayar ta gwamnati, an kara jaddada ta ga Kunigiyar da kuma kiranta domin cigaba da tattaunawa, Shugabancin Kungiyar Kwadago ya gana da safiyar yau ta yanar gizo domin duba sabuwar matsayar ta gwamnati.
“Bayan tattaunawa mai zafi, Shugabancin Kungiyar ya amince da hukuncin janye zanga-zangar da aka shirya yi a ranar 27 ga January da kuma wadda aka shirya yi ranar 2 ga Fabarairu na shekarar 2022.”
Wabba ya sanar da cewa, Kungiyar ta sanar da hukuncin nata ga sauran kungiyoyi da sukai tarayya da ita a goyon bayan ma’aikatan Najeriya wajen yunkurinsu na neman adalci.
Kungiyar ta kara tabbatar da matsayar ta na cewa, idan har aka cire tallafin mai, man zai yi tsada zuwa naira 320 da kuma naira 340 a kowacce lita.
Ta kara da cewa wannan zai kara ta’azzara hauhawar farashin kayayyaki a kasar, ya kara talauci, ya kara wahalar rayuwa ya kuma kara jefa miliyoyin ‘yan Najeriya cikin matsanancin yanayin rayuwa.