For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Kungiyar Kwadago Ta Sanya Sharadi Kafin A Cire Tallafin Mai

Manyan kungiyoyin kwadago a Najeriya sun zauna a jiya Talata inda suka fitar da sharuddan da Gwamnatin Tarayya za ta cika kafin a kyaleta ta cire tallafin man fetur.

Shugabannin Kungiyar ‘Yan Kasuwa, Kungiyar Kwadago, Kungiyar Ma’aikatan Sashin Man Fetur da Gas da sauransu, sun yi jawabai a Babban Taron Shekara tare da Kaddamar da Sabbin Shugabannin  Kungiyar Masu Siyar da Man Fetur ta Najeriya a Abuja.

Shugaban Kungiyar ‘Yan Kasuwa, Quadri Olaleye ya ce matsalar bangaren mai a Najeriya ta samo asali ne daga matsalar cin hanci da rashawa da rashin iya gudanar da gwamnati.

Ya ce, “tallafin mai da karin farashin mai wani abu ne da aka dade ana ta tattaunawa a kai. Najeriya ita ce kadai kasa a Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Mai, OPEC da take shigo da sama da kashi 90 zuwa 95 cikin 100 na tataccen mai don yi amfani da shi.

“Najeriya tana da matatun mai guda biyar, inda hudu daga ciki duk na gwamnati ne, sai kuma daya ta Kamfanin Albarkatun Mai na Niger Delta, NDPR.

“Za ku yi mamakin cewa, babu daya cikin matatun man gwamnati da yake aiki yanzu, a cikin shekaru 10 kacal da suka gabata, gwamnati ta yi asarar kusan dala biliyan 9.5 na kula da matatun da ba sa aikin.”

Olaleye ya tabbatar da cewa, Kungiyar ‘Yan Kasuwa ba ta adawa da cire tallafin mai matukar hakan zai samar da abin da ake bukata.

“Sai dai muna bukatar sanin me gwamnati za tai bayan cire tallafin,” in ji shi.

Shugaban Kungiyar ‘Yan Kasuwa, “ta yaya zamu gaskata gwamnati mu yarda cewa za su cire tallafin a wannan lokacin, saboda, a baya ma sun yi ikirarin cire abin da ake cewa ‘tallafi’, to tayaya za a cire abin da da ma an cire?

“Za a samu yi da kuma kula da matatun mai kamar yanda akai alkawari a baya aka kasa aiwatarwa? Za a samu gyaran matatun man da ake da su?

KU KARANTA: Rufe Twitter Ya Jawowa Najeriya Asarar Sama Da Naira Triliyan 10

“Me gwamnati za tai wajen magance dogaro da man da ake shigo da shi? Yana da muhimmanci a san wadannan tambayoyi, saboda muna da matukar bukatar sanin abin da gwamnati za tai kan wadannan, duk da rashin cika alkawarin gwamnati ya yi yawa.”

Kungiyar ‘Yan Kasuwar sun bukaci cewa, idan har aka cire tallafin, gwamnati ta sanya kudaden a bangaren da za su zama masu amfani ga tattalin arziki maimakon aiyukan da za su jawo asara.

“Ya kamata a samar da sabbin matatun mai masu aiki a kasar,” in ji Olaleye.

Ya kara da cewa, “dole ne a samar da kwakkwaran kwamiti domin ya binciki, daidaita tare da tabbatar da nasarar aiwatar da aiyuka da ma duk abubuwan da suka shafi haka.

“Matatun mai dole su yi aiki, sannan dole mu kawo karshen shigo da mai cikin kasa lokacin da za mu iya tacewa a cikin gida mu kuma siyar a kan farashin da ya dace.”

Ya ce, Najeriya tana da karfin iya samar da duk wadannan abubuwa har ma ta samu cigaba kamar sauran kasashen da suka ci gaba, “amma hakan ba zai faru ba, saboda ‘yan siyasarmu na yanzu ba sa son hakan ya faru.

“A karshe, idan wadannan bukatu ba su samu ba, hadaddiyar kungiyar kwadago,” in ji Quadri Olaleye.

Comments
Loading...