Daga: Abubakar Muhammad
Kungiyar Malamai ta Kasa NUT, reshen jihar jigawa ta zabi sabbin shugabannin da zasu ja ragamar kungiyar na tsawon shekaru 4.
A gun taron gwamna Muhd Badaru Abubakar wanda ya samu wakilcin mai bayarda shawara a kan harkokin kungiyoyin kwadago, Ibrahim Kyaumawa, ya bayyana cewa ilimi shi ne kashin bayan rayuwar al’umma a don haka gwamnatinsa ta rungumeshi a matsayin daya daga cikin abubuwa masu muhimmanci.
A jawabin maraba shugaban kungiyar mai barin gado Abdulkadir Inusa Jigawa, ya bayyana irin nasarorin da kungiyar ta samu a karkashin jagorancinsa.
Shi ma Shugaban kungiyar na kasa Nasir Idris wadda sakataren yada labaran kungiyar Audu T. Amma ya wakilta, ya yabawa yan kungiyar bisa halin dattako da suka nuna yayin gabatar da taron, ya kuma nuna farincikinsa ga gwamnatin jihar jigawa bisa yadda take dawayniya da kungiyar da kokarin gwamna na bunkasa ilimi da ma’abota ilimi.
Taken taron na bana shi ne “ilimantar da malamai domin cigaban kasa; matsaloli da kuma hanyoyi magance su”.
A lokacin taron, mafi yawan shugabannin kungiyar sun koma kan mukamansu ba tare da hamayyama ba wadanda suka hada da Abdulkadir Inusa a matayin shugaba, Dauda Shuaibu Guru a matsayin mataimaki, Sai kuma Bashir Abdullahi a matsayin mataimaki na 1 da kuma Aliyu Shehu Limawa a matsayin mataimaki na 2, Yayin da aka zabi Sadiya Haruna da Hussaina Yusuf a matsayin wakilan Mata.
A jawabin godiya shugaban kungiyar malamai ‘yan sa kai Ibrahim Abubakar, ya godewa mahalarta taron bisa nuna juriya da sanin yakamata a yayin gudanar da taron.