Shugabancin Kungiya Malaman Makarantun Polytechnics, ASUP, ta umarci mambobinta da su koma su ci gaba da aiki a ranar Litinin mai zuwa.
Wannan na zuwa ne bayan karewar wa’adin mako biyu na yajin aikin gargadi da kungiyar ta tsunduma a ranar 16 ga wannan wata na Mayu.
Sakataren Yada Labarai na Kungiyar ASUP na Kasa, Abdullahi Yalwa ne ya sanar da hakan a lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi a Abuja a yau Asabar.
Ya ce, an dau matakin ne a wani zaman tattaunawa na shugabannin kungiyar na kasa, inda aka duba yanayin yanda aka biya musu bukatun kungiyar.
Abdullahi Yalwa ya ce, Gwamnatin Tarayya ta biya hudu daga cikin bukatun kungiyar, inda ya kara da cewa, dakatar da yajin aikin ya samo asali ne domin a baiwa hukumomin da ke da ruwa da tsaki damar biyan sauran bukatun.
Ya baiyana fara biyan bashin kudaden sabon karin albashi mafi karanci a makarantun Polytechnics na Gwamnatin Tarayya a matsayin wani bangare na bukatun da aka biya musu.