Babbar kungiyar ‘yan kabilar Igbo, Ohanaeze Ndigbo, ta yabawa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bisa cika alkawarinsa na kammala aikin Gadar Niger ta Biyu kafin karewar wa’adinsa.
A wata sanarwa da aka fitar a jiya, Ohanaeze ta ce samar da gadar wani gagarumin aikin raya kasa ne da ke da tasiri ga zamantakewa da samar da tattalin arziki ba iya ga mutanen da ke kusa da gadar ba, har sauran mutanen Najeriya gaba daya.
A sanarwar da Sakataren Yada Labarai na Kasa na kungiyar, Dr. Alexander Ogbonnia ya sanyawa hannu, kungiyar ta tuna cewa, bukatar samar da Gadar Niger ta Biyu ta zama dole ne jim kadan bayan kammala Yakin Basasa na Najeriya.
Ya ce, “An kaddamar da gadar farko ta Niger ne a shekarar 1965, sannan kuma Yakin Basasar Najeriya ya fara a 1967. Saboda haka ita wannan gadar ba ta tsira ba daga hare-haren yaki a lokacin.
“Gadar Niger ta Biyu ta kasance babbar bukatar al’ummar Igbo cikin sama da shekaru 50 da suka wuce saboda dalilai biyu; baya da cunkuson ababan hawa a kan gadar farko, babban abin tsoron shine, akwai tsattsagewa a gadar wanda nauyin da take dauka ka iya sawa ta ruguje ta dulmiyar da motoci da kayan kansu cikin kogin Niger.”
“Saboda kiraye-kirayen a samar da Gadar Niger ta Biyu, tsohon shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida, a shekarar 1992, ya kalubalanci injiniyoyin Najeriya da su zana gadar.”
Ya kuma kara da cewa, gwamnatoci da dama sun yi anfani da Gadar Niger ta Biyu domin samun dama a wajen ‘yan kabilar Igbo, musamman ma a lokacin yakin neman zabe.
“Lokacin da Shugaban Kasa Buhari ya yi alkawarin cewa zai kammala aikin Gadar Niger ta Biyu, da yawa ba su yarda ba, musamman duba da yanda bai boye nade-naden mukamansa da rabon arzikin kasa na nuna wariya ga yakin Kudu maso Gabas ba,” in ji shi.