For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

KWALLON KAFA A JIGAWA: Hussaini Mohammed Rally Da Kokarin Inganta Rayuwar Matasa

Wani abu da ya ja hankali na a kan wannan batu shine, yunkurin da wasu matasa suka yi min da na zo dan zama jagoran shugabannin kungiyar su ta kwallon kafa, sai na nuna musu a’a ganin cewar ni bani da kwarewa dama cikkekken nazari a kan al’amuran da suka shafi wasanni musamman na grass root (kasa-kasa), kawai ni dai ina da sha’awar wasannin da kuma burin yadda wasanni, musamman kwallon kafa zai taimakawa rayuwar matasanmu, domin shi suka fi maida hankali a kai.

Karamin bincike da nazarin da na yi ne musamman a kan cigaban wasan kwallon kafa na ga ya kamata mu yi tsokaci a kai don muhimancin rayuwar matasanmu da kuma dacewar masu hali su shigo don tallafawa wasanni a jiharmu. Domin duk inda aka sami ci gaba a harkar matasa to al’ummarsu sun tallafa musu.

Wani abin mamaki da ban sha’awa shine yadda na ga kananan clubs wato kungiyoyi na unguwanni suna sabunta yarjejeniya ta saye da sayarwar ýan wasa, da ma bayar da aron ýan wasa transfer market, wand a da hatta wasanni a tsakanin wadannan kungiyoyi ba a cika wanye wa lafiya ba. Nazari ya nuna cewa wanan ci gaba ya zo ne bayan da da shi Hussaini Rally ya assasa da daukan nauyin league a kannan hukumomin Jigawa ta gabas da wasu daga cikin kananan hukumomi a sauran yan kunan Jigawa.

Nazari da bincike ya nuna akwai a kalla kimanin kungiyoyi (clubs) sama da 150 na matasa da suke fafatawa a wasanin league.

A yanzu ma kanan hukumomin Guri, Auyo, K/Hausa, K/Kasamma, Birniwa da Hadejia duka suna fafatawa a gasar primier da ya assasa, a kalla kowace karamar hukuma a kwai clubs 20 da suke wannan gasa, tunanin wadannan wasanni ba kawai motsa wasan kwallo bane harma da taimakon matasan don samun rayuwa mai inganci.

A karamar hukumar Hadejia kadai ana gasar wasanni guda hudu, clubs 28 ne suke fafatawa a gasar Professional League, 20 suke buga Premiere League, clubs 22 suke buga League 1 sannan kuma clubs 26 suke fafatawa a gasar League 11. Wannan wasanni ya kara zaman lafiya da zumunta a tsakanin mutanen wannan yankin.

A bin mamaki tsarin da ake league kamar a Karamar Hukumar Hadejia tamkar a kasashen turawa, a kwai rukunin da suke buga Premier League, Nationwide I & II, wannan ya dawo da tarbiyar wassan kwallo a tsakanin matasanmu, ya kuma bude hanyar dorewa da wasan kwallo ya zama sana’a a tsakanin matasanmu.

Bincike ya nuna wasu da ga cikin matasan a yau suna buga kwallo a manyan kungiyoyin kwallo na Nigeria a matsayin professionals, wasu ma sun zaman to coaches wato masu horaswa, wasu kuma sun zama kwararrun alkalan wasa, wannan kadai ba karamin dan ba bane wajen farkar da al’umma da shugabanni cewar za’a iya tallafawa matasa don samun sana’a ta hanyar wasannin.

A bin sha’awa ma shine yadda yawan wasanni da kuma tsarin da a ka saka na cigaban wasanni a yau, ya taimaka gaya wajen canjawa matasanmu tunani a kan ta’ammali da miyagun kwayoyi, karamin bincike a tsakanin matasanmu ya nuna cewa, wasannin da matasa suke fafatawa a kai, ya zama dole sai matasa suna kykkyawan atasaye da cikekkiyar lafiya in har matashi yana son nuna bajintar sa da kuma cika burin son a zama kwararren dan kwallon kafa. Yawan wasanni ya sanya matasa barin ta’ammali da miyagun kwayoyi da kuma hikimar yakar maye ta hanyar wasanni.

Karatun matasa, wani abu da Hussaini ya kawo a shigarsa alámarin kwallon kafa shine, wajen mai da matasa da yawa makarantu domin su ci gaba da karatunsu, ya yi haka ne wajen basu kyakkywar shawara da mai da su makarantu, basu kwarin gwiwa dama tallafa musu.

A ci gaban wasan kwallon kafa a Jigawa, kungiyar da Hussaini Rally ya assasa ta HALFA sama da shekaru uku wannan kungiyar tana daga cikin kungiyoyin da suke buga wasanni kwararru a Najeriya wato Professional League, wato Nigerian Nationwide League.

Wasu yan wasa daga cikin wannan kungiyar a yau suna bugawa manyan kungiyoyi a Najeriya, wasu na fafutukar fita kasashen waje, wannan ba karamin ci gaba a ka samu a harkar wasanni ba a Jigawa.

Ahmed Ilallah ya rubuto daga Hadejia, Jihar Jigawa
alhajilallah@gmail.com

Comments
Loading...