For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Kwamitin Samar Da Sabon Mafi Ƙarancin Albashi Ya Miƙa Rahoton Kammala Aikinsa Ga Gwamnatin Tarayya

A jiya Litinin, Kwamitin Samar da Sabon Mafi Ƙarancin Albashi ya miƙa rahotonsa ga Sakataren Gwamnatin Tarayya bayan kammala aikinsa.

Daraktan Sadarwa da Hulɗa da Jama’a na ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Segun Imohiosen ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya sanya wa hannu.

Ya bayyana cewar za a miƙa rahoton ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu domin ɗaukar matakin da ya dace a lokacin da shugabannin ƙungiyar ƙwadago da wakilan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu suka dawo Najeriya daga taron Ƙungiyar Ƙwadago ta Duniya da ke gudana yanzu haka a Geneva, Ƙasar Switzerland.

Sanarwar ta bayyana cewar, Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume ya godewa Shugaban Kwamitin, Bukar Goni Aji da mambobin kwamitin kan ƙoƙarin da suka yi.

Shugaba Tinubu dai ya naɗa wannan kwamiti mai mutane 37 ne a ranar Talata, 30 ga watan Janairun bana, kamar yanda Dokar Samar da Mafi Ƙarancin Albashi ta 2019 ta tanada.

An ɗorawa kwamitin nauyin bayar da shawara kan sabon mafi ƙarancin albashin da za a na biyan ma’aikata da ke aikin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu a Najeriya.

Comments
Loading...